Ƙasashen duniya na ci gaba da fuskantar tangarɗar samar da makamashi yayin da ƙasar Japan ta fara tuntuɓar masu samar da ɗanyen mai, ciki har da Najeriya, domin tabbatar da wadataccen mai a cikin gida.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa, wannan mataki na zuwa ne sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da ya dagula kasuwar mai ta duniya.
Mataimakiyar darakta janar ta ma’aikatar tattalin arziƙi da masana’antu ta Japan, Narumi Hosokawa, ta ce ƙasar na kuma duba yiwuwar shigar da mai daga Malaysia, Azerbaijan, Brazil da Angola.
Ta bayyana cewa ana ƙoƙarin rage dogaro da yankin Gabas ta Tsakiya wanda ke samar da kusan kashi 95 na man ƙasar a halin yanzu.
Firaminista Sanae Takaichi ta sanar a wani taron majalisar ministoci cewa, za a fitar da ajiyar mai na kwanaki 20 daga watan Mayu.
Ta ce ƙasar na shirin tabbatar da cewa sama da rabin man da take shigarwa da shi zai riƙa zuwa ne ta hanyoyin da ba su haɗa da mashigin Hormuz ba.
A cewar bayanai, Japan na da ajiyar mai na tsawon kwanaki 228 zuwa ranar 7 ga Afrilu, ciki har da kwanaki 143 a na ma’ajiyar gwamnati, sabon sakin man yanzu zai fito daga cikinta.
Rahoton ya ƙara da cewa ƙasar na ƙara yawan sayen mai daga Amurka, inda ake sa ran wannan adadi zai ninka sau huɗu a watan Mayu idan aka kwatanta da bara.
Wannan mataki na nuni da yadda ƙasashe ke ƙoƙarin kare tattalin arziƙinsu a lokacin rikici.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu tsakanin Amurka da Iran, har yanzu ana fuskantar barazana a mashigin Hormuz, lamarin da ke janyo cikas ga samar da makamashi a duniya baki ɗaya.