Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya bayyana Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin marasa tsari sakamakon sauya jam’iyyu da suke yi akai-akai.
Morka ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira a shirin The Morning Brief na Channels Television.
Ya yi martani ne kan sauya sheƙar da Obi da Kwankwaso suka yi daga jam’iyyar ADC zuwa NDC a ranar Lahadi.
Shugabannin ƴan adawar sun ce sun bar ADC ne sakamakon yawan shari’o’in cikin gida da suka danganta da matsin lamba daga jam’iyya mai mulki.
Sai dai Morka ya musanta zargin, yana mai cewa APC ba ta da hannu a rikice-rikicen jam’iyyun adawa.
Ya ce shugabannin biyu na neman dandamali ne mai sauƙi domin samun tikitin takarar shugaban ƙasa kawai.
Morka ya ce “waɗannan mutane ba su da wani tsari, suna ta gudu daga wannan jam’iyya zuwa wata maimakon gabatar da manufofi.”
Ya kuma zargi Obi da saɓa wa kalamansa na baya da ke sukar masu sauya jam’iyya domin anfani na siyasa.
A cewarsa, APC ba ta da buƙatar tsoma baki a rikicin ADC, yana mai cewa jam’iyyar na fama da saɓanin ra’ayi ne tsakanin mambobinta.
Channels Television ta rawaito cewa Obi da Kwankwaso sun karɓi katin zama ƴan NDC a hannun jagoran jam’iyyar, Seriake Dickson.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027 a Najeriya.