Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta sanar da jadawalin gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani na shekarar 2026 tare da bayyana farashin fom ɗin shiga takara.
A cikin sanarwar da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, an bayyana cewa, sayar da fom ɗin zai gudana daga 5 zuwa 10 ga Mayu, 2026.
An ce mayar da fom ɗin da aka cika zai kasance daga 11 zuwa 13 ga Mayu, yayin da tantance ƴan takara za ta gudana daga 14 zuwa 15 ga watan.
Sakamakon tantancewar za a fitar da shi a ranar 17 ga Mayu, yayin da sauraron ɗaukaka ƙara zai gudana daga 18 zuwa 19 ga watan.
Za a fitar da jerin sunayen waɗanda suka tsallake a ranar 20 ga Mayu, kafin fara zaɓuɓɓukan fidda gwani daga 21 ga watan.
Zaɓen kujerun majalisun jihohi da na tarayya zai gudana a rana guda, yayin da na gwamna zai kasance a ranar 22 ga Mayu.
An tsara zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a ranar 25 ga Mayu, kafin taron kwamitin zartarwa na ƙasa a ranar 26 da babban taron jam’iyya a ranar 27 ga watan.
Jam’iyyar ta ce kuɗin fom na shugaban ƙasa ya kai naira miliyan 100, na gwamna miliyan 50, na sanata miliyan 20, na wakilai miliyan 10, da na majalisar jiha miliyan 3.
Ta kuma ce za ta bayar da rangwame kashi 50 ga matasa da kashi 25 ga mata da masu naƙasa domin ƙara ƙarfafa shigar su.