Tinubu ya naɗa sabon minista, ya kuma kafa kwamiti domin gyaran wutar lantarkin Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya sanar da naɗin Joseph Tegbe a matsayin Ministan Wutar Lantarki tare da naɗa Lanre Babalola a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan wutar lantarki a Abuja.

Sanarwar ta fito ne cikin takardu biyu daga Fadar Shugaban Ƙasa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.

A cewar fadar shugaban ƙasar, naɗin Tegbe ya biyo bayan murabus ɗin tsohon ministan wuta, Adebayo Adelabu, wanda ya sauƙa domin neman takarar gwamna a Jihar Oyo.

An bayyana Joseph Tegbe a matsayin ƙwararre a fannin tattalin arziƙi da harkokin kuɗi da ke da fiye da shekaru 35 na gogewa a ɓangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Rahoton fadar shugaban ƙasar ya nuna cewa Tegbe ya taɓa zama babban abokin hulɗa a kamfanin KPMG Africa inda ya jagoranci ayyuka na gyaran manufofin kuɗi da tsarin hukumomi.

A halin yanzu, Tegbe shi ne Darakta-Janar kuma mai kula da hulɗa ta ƙasa da ƙasa a shirin haɗin gwiwar Najeriya da ƙasar Sin.

Fadar shugaban ƙasar ta ce naɗin nasa zai taimaka wajen daidaita tsarin lantarki, inganta aiki da kuma jawo zuba jari mai dogon zango a ɓangaren.

Bayo Onanuga ya ce, “Shugaban ƙasa na sa ran sabon ministan zai kawo ƙwarewarsa domin inganta sakamakon da ake samu a ayyuka a ɓangaren wutar lantarki.”

A wani ɓangare, shugaban ƙasar ya naɗa tsohon ministan wuta, Lanre Babalola, a matsayin shugaban kwamitin musamman na gyaran ɓangaren wutar lantarki.

Fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa Babalola na da cikakkiyar masaniya kan ƙalubalen da ke tattare da ɓangaren wutar lantarki a Najeriya.

Sanarwar ta ce naɗin nasa na nuna ƙudurin gwamnati na kawo sauyi mai inganci a ɓangaren ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda.

Hakazalika, gwamnatin ta sauya sunan ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan makamashi da Olu Verheijen ke jagoranta zuwa mai kula da mai da iskar gas.

A cewar Onanuga, an ɗauki matakin ne domin fayyace ayyuka da kauce wa maimaita nauyin aiki a tsarin tafiyar da harkokin makamashi.

Sabon kwamitin da aka kafa zai mayar da hankali kan rage asarar lantarki, inganta kuɗaɗen shiga da kuma bunƙasa amfani da wuta a ɓangarori daban-daban.

An kuma ce kwamitin zai gabatar da tsarin aiki na kwanaki 90 domin aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa a ɓangaren lantarkin.

Fadar shugaban ƙasar ta ƙara da cewa ana sa ran waɗannan matakai za su kawo ci gaba a samar da wutar lantarki da inganta rayuwar al’umma a Najeriya.

LantarkiNajeriyaTinubu
Comments (0)
Add Comment