Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun bayyana damuwa kan ƙaruwar rashin tsaro da talauci a wani taron gabatar da jawabi kafin bikin ranar ma’aikata ta 2026 da aka gudanar a Abuja.
Kwafin jawabin da aka fitar a daren ranar Alhamis ya nuna cewa shugabannin sun yi gargaɗin cewa matsalolin tattalin arziƙi na ƙara lalata walwalar ma’aikata da samar da aiki mai inganci.
Shugaban ƙungiyar Nigeria Labour Congress, NLC, Joe Ajaero, ya ce rashin tsaro da talauci sun zama manyan ƙalubale ga samar da aikin yi mai kyau a ƙasar.
A cewarsa, miliyoyin ƴan Najeriya na rayuwa cikin talauci yayin da ingantattun ayyukan yi ke raguwa a ƙasar.
Joe Ajaero ya ce, “Idan aka kawar da rashin tsaro yau, za a samu abinci a ko’ina domin mutane za su koma gonakinsu.”
Ya ƙara da cewa kusan kashi 90 cikin 100 na ayyukan yi a Najeriya na cikin ɓangaren da ba na hukuma ba, inda babu tsaro ko tsarin fansho ga ma’aikata.
Sai dai ya yabawa gwamnatin tarayya kan dawo da biyan kuɗin gratuti ga ma’aikata bayan ritaya.
Shi ma shugaban Trade Union Congress, TUC, Festus Osifo, ya buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin ma’aikata domin yaƙar talauci da rashin tsaro.
Ya ce, “Neman tsarin aikin yi mai kyau ba abin da za a yi sassauci a kai ba ne ga ma’aikatan Najeriya.”
A nasa ɓangaren, farfesa a fannin nazarin dangantakar ƙasa da ƙasa, Kunle Olawunmi, ya ce talauci da rashin tsaro na barazana ga ci gaban Najeriya.
Ya bayyana cewa ba za a iya gina tattalin arziƙi mai ƙarfi ba a cikin al’ummar da ke fama da tsoro da yunwa.
Kungiyar Federation of Informal Workers Organisations of Nigeria ta buƙaci gwamnati ta samar da tsarin tallafin jin ƙai ga ma’aikatan ɓangaren da ba na hukuma ba.
A cewar ƙungiyar, sama da kashi 93 cikin 100 na ma’aikatan Najeriya na cikin wannan ɓangare amma ba sa cin gajiyar tsarin fansho da na kula da lafiya.