Jam’iyyar Labour Party (LP) ta zaɓi tsohuwar ministar kuɗi, Nenadi Usman, a matsayin shugabar jam’iyyar ta ƙasa a babban taron da aka gudanar a ranar Talata a Umuahia, babban birnin Jihar Abia.
Sanarwar da sabon kakakin jam’iyyar, Ken Asogwa, ya fitar ta tabbatar da cewa an zaɓi Nenadi ne bayan ta riƙe muƙamin shugabar kwamitin riƙon ƙwarya kafin wannan lokaci.
An naɗa ta shugabar kwamitin riƙon ƙwarya ne a ranar 4 ga Satumba, 2024, a taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka yi a Umuahia bayan ƙarewar wa’adin shugabannin baya.
Rahotanni sun nuna cewa, ta jagoranci jam’iyyar cikin rikice-rikicen shugabanci har zuwa lokacin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da sahihancin shugabancinta a ranar 21 ga Afrilun nan.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta riga ta amince da ita a matsayin shugabar riƙon ƙwarya a ranar 30 ga Janairu, bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya na ranar 21 ga Janairu.
A jawabin karɓar muƙamin, Nenadi Usman ta gode wa ƴan jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna mata tare da alƙawarin sake farfaɗo da jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Ta kuma yabawa gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, kan shugabanci nagari tare da jaddada ƙudurinta na tabbatar da haɗin kai da sulhu a cikin jam’iyyar.
A nasa ɓangaren, Alex Otti ya buƙaci sabbin shugabannin jam’iyyar su samar da ingantaccen shugabanci da kuma ƙarfafa tsare-tsaren jam’iyyar a faɗin ƙasar.
Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Iheanacho Obioma a matsayin sakatare na ƙasa, Nike Oriola mataimakiyar shugaba, da Ken Asogwa a matsayin sakataren yaɗa labarai.
Haka kuma an rantsar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) kuma sun fara aiki nan take.