Ƙungiyar Grassroots Mobilization for Asiwaju and Danmodi/Roller (GMA/DR 2023) ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, tare da amincewa da tsayar da Ambasada Dakta Halima Suleiman Zakari takarar Sanata, a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 29 ga Afrilu, 2026.
Shugabannin ƙungiyar, Kwamared Aminu Aminu da Abdulrashid Ali Zareku, sun bayyana cewa manufar taron ita ce nuna godiya da kuma bayyana goyon baya ga shugabannin da suka nuna jajircewa wajen bunƙasa ƙasa da Jihar Jigawa.
A cikin sanarwar, sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan manufofinsa na “Renewed Hope Agenda”, suna masu cewa, sun taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da ƙarfafa hukumomi a ƙasar.
“Mun yaba da irin matakan da gwamnati ke ɗauka domin mayar da Najeriya kan turbar ci gaba mai ɗorewa,” in ji ƙungiyar.
A matakin jiha kuwa, ƙungiyar ta goyi bayan sake zaɓen Gwamna Umar Namadi karo na biyu, tana mai cewa manufofinsa sun inganta harkokin ilimi, lafiya, noma da ababen more rayuwa a Jigawa.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa, salon shugabancin gwamnan na mayar da hankali kan jama’a ya taimaka wajen inganta rayuwar al’umma a faɗin jihar.
Haka kuma, ƙungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Ambasada Dakta Halima Suleiman Zakari domin tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Jigawa ta Tsakiya.
A cewar ƙungiyar, Halima Zakari ta nuna ƙwarewa da jajircewa ta hanyar aiwatar da ayyukan jin ƙai, tallafin ilimi da sauran shirye-shiryen bunƙasa al’umma.
Ƙungiyar ta ce, za ta ɗauki nauyin sayen fom ɗin takararta idan ta samu tikitin jam’iyya, a matsayin alamar nuna goyon baya gare ta.
Shugabannin sun kuma yi kira ga al’umma da masu ruwa da tsaki su mara wa waɗannan shugabanni baya domin ci gaban ƙasa da Jihar Jigawa.
Sun ƙara da cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a cikin lumana domin ƙarfafa demokaraɗiyya da haɗin kai a Najeriya.