Iran ta buƙaci a biya ta diyya kan ɓarnar da hare-haren Amurka da Isra’ila suka haddasa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sasanta rikicin a yankin.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce ƙasashe biyar na yankin ne zasu biya diyyar, yana zargin cewa an yi amfani da ƙasashensu wajen kai hare-haren.
Gwamnatin Iran ta kuma gabatar da shawarar samar da tsarin karɓar haraji ga jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigin Hormuz domin samar da kuɗin diyya.
Mai magana da yawun gwamnati, Fatemeh Mohajerani, ta ce an ƙiyasta cewa ƙasar ta yi asarar kusan dala biliyan 270 tun bayan fara rikicin a ranar 28 ga Fabrairu.
Ta ƙara da cewa an tattauna batun diyya a tattaunawar baya-bayan nan tsakanin Tehran da Washington, kuma za a sake duba shi a tattaunawa mai zuwa.
Gwamnatin ta ce har yanzu tana nazarin ɓarnar da aka yi wa muhimman kayayyakin more rayuwa ciki har da masana’antun mai da iskar gas, da tashoshin wutar lantarki da hanyoyin sufuri.
Rahotanni sun nuna cewa, asibitoci, makarantu da gidajen fararen hula da dama sun lalace ko sun rushe sakamakon hare-haren.
A cewar gwamnati, halin tattalin arziƙi na yanzu ba ya ba ta damar biyan diyya ga ƴan ƙasa da gidajensu suka lalace.
Haka kuma, jami’an harkokin jiragen sama sun ce jiragen farar hula 60 sun lalace, ciki har da 20 da aka lalata gaba ɗaya, yayin da sauran ke fuskantar matsalar kayan gyara sakamakon takunkumi.
An kuma ce asarar kuɗaɗen shiga ta kamfanonin jiragen sama ta zarce rial tiriliyan 300 a cikin kwanaki 40 na yaƙin.
Duk da wannan, jami’an Iran sun jaddada cewa ba za su sassauta matsayinsu ba a tattaunawa da Amurka, musamman kan batun shirinta na nukiliya.