Kafar watsa labarai ta BBC ta sanar da shirin rage ma’aikata tsakanin 1,800 zuwa 2,000, wanda ke kusan kashi ɗaya cikin goma na ma’aikatanta, domin fuskantar matsin tattalin arziƙi mai tsanani da yake ciki.
BBC ta ce tana buƙatar tanadin fam miliyan 500 cikin shekaru biyu masu zuwa, lamarin da ya jawo yiwuwar rufe wasu tashoshi ko dakatar da wasu ayyuka, a cewar muƙaddashin babban darakta Rhodri Talfan Davies.
Davies ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Media Show na Radio 4, inda ya ce dole ne a ɗauki matakai masu tsauri amma cikin lura.
Ya ce za a bayar da ƙarin bayani daga baya a wannan shekara kan yadda rage ayyukan zai shafi ayyukan kafar.
A cikin saƙon da ya aika wa ma’aikata, ya ce kamfanin na fuskantar giɓin kuɗi tsakanin kashe kuɗi da samun kuɗin shiga, wanda ke ƙaruwa saboda hauhawar farashin samar da shirye-shirye.
Ya ƙara da cewa kuɗin lasisin BBC da kuɗaɗen kasuwanci suna fuskantar matsin lamba daga tattalin arziƙin duniya da ke cikin rikici.
Ƙungiyoyin ma’aikata sun bayyana damuwa, inda Bectu ta ce rage ma’aikata irin wannan zai yi illa sosai ga ma’aikata da kuma aikin BBC baki ɗaya.
Ƙungiyar NUJ kuma ta ce matakan za su haifar da rashin tabbas da wahala ga ma’aikata tare da rage ingancin aikin jarida.
BBC na ci gaba da tattaunawa da gwamnati kan makomar kuɗin lasisi kafin sabunta yarjejeniyar sarauta a ƙarshen 2027.