Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta kammala babban taronta na ƙasa a ranar Talata a Abuja inda wakilai suka kaɗa ƙuri’a da samun gagarumin rinjaye domin gyara kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Shugaban kwamitin zaɓe na jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ne ya sanar da sakamakon bayan kammala kaɗa ƙuri’ar.
Ya ce an tantance wakilai 1,576, yayin da aka soke ƙuri’u 11, inda wakilai 1,471 suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da gyaran, wanda ya kai kashi 94 cikin ɗari na dukkan wakilan.
A cewarsa, sakamakon ya tabbatar da cewa taron ya amince da gyaran kundin tsarin mulkin jam’iyyar a hukumance.
Kafin fara kaɗa ƙuri’a, shugaban kwamitin shari’a da shirye-shiryen taro, Olumide Apata, ya jagoranci amincewa da muhimman shawarwari daga tarukan NEC na 97, 98 da 99.
Sakataren tsare-tsare na ƙasa, Chinedu Idigo, ya bayyana cewa an amince da sassauta sharuɗɗan zama mamba da kuma dakatar da tsarin raba muƙamai bisa yankuna.
Haka kuma taron NEC na 99 ya rusa kwamitin gudanarwa na ƙasa ƙarƙashin Ralph Nwosu, tare da bai wa sabon kwamitin ƙarƙashin David Mark cikakken iko, matakin da babban taron ya tabbatar.
A jawabin rufewa, shugaban jam’iyyar na ƙasa, David Mark, ya yabawa yadda aka shirya taron, yana mai cewa ya fi sauran tarukan da ya halarta a baya tsari.
Ya ce taron ya zama farkon tafiyar jam’iyyar zuwa fadar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
A yayin taron kuma, jam’iyyar ta sanar da korar wasu mambobi ciki har da Nafiu Bala da ɗan majalisar wakilai Leke Abejide bisa zargin ayyukan da suka saɓa wa manufofin jam’iyyar.
Taron ya kuma samu jawabai daga manyan ƴan siyasa ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola, waɗanda suka bayyana damuwarsu kan batutuwan tsaro, tattalin arziƙi da gudanar da gwamnati.