Abubuwan da suka faru a shekaru uku na yaƙin basasar Sudan na ci gaba da ta da hankalin duniya

Ranar 15 ga Afrilu ta cika shekaru uku da ɓarkewar yaƙin basasa a Sudan tsakanin rundunar sojin ƙasar da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF).

Rikicin, wanda ya samo asali daga taƙaddama kan iko tsakanin Abdel Fattah al-Burhan da Mohamed Hamdan Dagalo, ya tilasta wa fiye da mutane miliyan 14 barin muhallansu, lamarin da ya haifar da ɗaya daga cikin manyan matsalolin jin ƙai a duniya, kamar yanda Al Jazeera ta rawaito.

A cewar kungiyar Armed Conflict Location & Event Data (ACLED), sama da mutane 50,000 ne aka tabbatar sun mutu a cikin shekaru ukun, duk da cewa ana kyautata zaton adadin ya fi haka idan aka haɗa da waɗanda suka mutu sakamakon cututtuka da yunwa.

Ƙungiyar ta ce daga ranar 15 ga Afrilu 2023 zuwa 27 ga Maris 2026 an samu hare-hare aƙalla 13,401, wanda ya kai matsakaicin hare-hare 12 a kowace rana.

Rahoton ya nuna cewa, rundunar sojin Sudan ce ke da alhakin kashi 53 cikin ɗari na hare-haren, yayin da RSF ta kai kashi 35, sauran kuma wasu ƙungiyoyi ne suka aikata.

An ce hare-haren sun haɗa da fafatawa da makamai, hare-haren sama da jirage marasa matuƙi, harbe-harbe da kuma lalata dukiyoyi.

Rikicin ya fara ne a birnin Khartoum inda RSF ta ƙwace manyan sassan birnin kafin daga bisani ta bazu zuwa yankunan Darfur da Gezira.

A shekarar 2024, yaƙin ya koma na tsawon lokaci tare da fafatawa kan iko da yankuna, kafin sojojin Sudan su ƙwato wasu sassan Omdurman a ƙarshen shekarar.

A watan Mayun 2025, sojojin Sudan suka kafa gwamnatin farar hula a Port Sudan, yayin da RSF ta kafa nata a Nyala, lamarin da ya ƙara raba ƙasar gida biyu.

Zuwa shekarar 2026, ƙasar ta kasu gida biyu inda sojoji ke iko da gabas da tsakiyar yankuna, yayin da RSF ke riƙe da Darfur da wasu sassan Kordofan.

Birnin Khartoum ya fi kowanne yanki shan hare-hare, inda aka samu sama da hare-hare 5,600, kafin sojoji su sake ƙwato shi a shekarar 2025.

AfricaRSFSudan
Comments (0)
Add Comment