Majalisar ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ta buƙaci Musulmi su yi addu’ar cire shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan.
A wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar Litinin, babban sakataren majalisar, Nafiu Baba-Ahmad, ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe.
Ya ce majalisar ta samu tambayoyi da dama kan lamarin, wanda ya samo asali daga “labaran bogi da ba su da tushe.”
Ya ƙara da cewa, “A bayyane yake cewa majalisar ba ta taɓa bayar da irin wannan umarni ba a kowane lokaci.”
Majalisar ta ce irin waɗannan labarai an ƙirƙiro su ne domin jefa ta cikin rikicin siyasa.
“Wannan yunƙuri ne na jefa mu cikin rikicin siyasa mai raba kan jama’a,” in ji Ahmad.
Sai dai duk da haka, majalisar ta sake jaddada matsayinta na cewa shugaban INEC ya sauƙa ko a cire shi, bisa damuwa kan rashin adalci da gaskiyarsa.
Ta ce wannan matsayi ba ya da alaƙa da siyasa ko ɓangaranci.
Majalisar ta kuma gargaɗi jama’a da su guji yarda da labarai daga hanyoyin da ba a tabbatar da su ba, tana mai cewa hakan na haddasa ruɗani da raba kan al’umma.
Ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da inganta zaman lafiya da adalci a ƙasa.