Peter Obi Ya Yi Gargaɗi Kan Sake Zaɓen Tinubu a 2027 Saboda Gazawa a Wutar Lantarki

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, yana mai zargin gazawarsa wajen cika alƙawarin samar da isasshiyar wutar lantarki.

Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai tunatar da alƙawarin da Tinubu ya yi a 2023 cewa, “idan ban samar da wutar lantarki mai isasshiya ba cikin shekaru huɗu, kada ku sake zaɓena”.

Ya ce a lokacin da gwamnatin ta hau mulki, samar da wutar lantarki ya haura megawatt 4,000, amma yanzu ya ragu ƙasa da haka duk da ƙarin kuɗin wuta da ƴan kasa ke biya.

A cewarsa, “yanzu Najeriya na da mafi ƙarancin amfani da wutar lantarki a duniya, ƙasa da kashi 30 cikin 100 na matsakaici a nahiyar Afirka”.

Obi ya kuma soki kalaman shugaban ƙasa yayin wata ziyara a Jos, inda ya ce, “ba ku da wuta a nan, zan koma cikin mintuna goma,” yana mai cewa hakan na nuna rashin tausayi ga halin da jama’a ke ciki.

Ya ƙara da cewa, “lokaci ya yi da za a daina zaɓen shugabanni marasa ƙwarewa da tausayi,” yana mai kira ga al’umma su ɗauki mataki.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalar wutar lantarki a faɗin Najeriya, lamarin da ke shafar tattalin arziƙi da rayuwar yau da kullum.

LantarkiPeter ObiTinubu
Comments (0)
Add Comment