Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce ana iya kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya cikin watanni shida idan gwamnatin tarayya ta nuna cikakken ƙudurin yin hakan.
Ndume ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a tashar Channels Television a shirin Politics Today ranar Litinin.
Ya nuna damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa musamman a yankin Arewa maso Gabas.
A cewarsa, abin da ake buƙata ba ƙorafi ba ne, sai dai ɗaukar mataki mai ƙarfi da nuna niyyar shugabanci.
Ya ce, “idan shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya sun ɗauki lamarin da muhimmanci, za a iya kawo ƙarshen matsalar cikin watanni shida.”
Sanatan ya jaddada cewa dole ne a horar da sojoji da kyau, a basu kayan aiki da makamai, tare da ƙarfafa musu gwiwa.
Ya kuma nuna damuwa kan yawan asarar sojoji, ciki har da manyan jami’ai, yana mai cewa hakan na nuna akwai matsaloli a tsarin aikin da ake yi.
Ndume ya ce rashin cikakkiyar aiwatar da tsare-tsaren tsaro na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta’azzara matsalar.
Game da taimakon ƙasashen waje, ya ce abin da ake buƙata shi ne fasaha da bayanan sirri da ƙwararru, ba wai a dogara da sojojin ƙasashen waje ba.
Ya ƙara da cewa amfani da na’urorin zamani kamar jiragen sama marasa matuƙa na iya taimakawa wajen rage hare-haren cikin sauri.
Bayanin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tsaro a ƙasar, bayan rahotannin harin bam a kasuwar Jilli da kuma harin da aka kai sansanin soji a Benisheikh.
Gwamnatin Najeriya da rundunar sojin sama sun ce suna binciken rahotannin da ke nuna cewa harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.