Ƴan sanda sun kama jami’ansu 6 kan zargin garkuwa da mutane da ƙwatar kuɗaɗe

Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta kama wasu mutane tara, ciki har da jami’anta shida, kan zargin garkuwa da mutane da karɓar kuɗi da ƙarfi.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikioyedem, ta ce waɗanda ake zargin sun haɗa da jami’ai masu aiki da wani da aka kora.

Ta ce suna amfani da kayan ƴan sanda domin yaudarar jama’a a birnin Benin.

A cewarta, suna kama mutane ne a hanya sannan su tilasta musu cire kuɗi ta hanyar POS.

Ta bayyana cewa sun gudanar da ayyukansu ne a yankin Teboga kusa da Aduwawa.

Kamen nasu ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama’a suka riƙa yi kan irin waɗannan hare-hare.

Binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar na aiki ne cikin tsari tare da amfani da kayan aikin ƴan sanda.

Rundunar ta ce ana ci gaba da ladabtar da jami’an da ke aiki, kuma za a gurfanar da su a kotu idan an kammala bincike.

Ikioyedem ta ce lamarin ya ɓata sunan rundunar ƴan sanda sosai. Ta kuma gargaɗi masu POS da su guji taimaka wa aikata laifi, tana mai cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu.

'Yan SandaNajeriyaTsaro
Comments (0)
Add Comment