Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƴan Kasuwa a Najeriya (TUC) ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kuɗaɗen ƙarin kuɗin shiga na mai domin tallafawa matatun mai na cikin gida su rage raɗaɗin hauhawar farashin fetur ga ƴan kasa.
Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya gargaɗi cewa farashin litar fetur na iya kaiwa Naira 2,000 idan ba a ɗauki mataki ba.
Ya ce hauhawar farashin na ƙara jefa ma’aikata cikin mawuyacin hali.
Osifo ya danganta matsalar da sauye-sauyen farashin ɗanyen mai a duniya da kuma faɗuwar darajar naira.
Ya kuma ce rikice-rikicen ƙasa da ƙasa, musamman tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, na taka rawa wajen dagula samar da mai.
Ya ba da shawarar cewa a riƙa amfani da kuɗaɗen da ake samu na ribar sama da yanda aka ƙiyasta a kasafin kuɗin gwamnati wajen tallafawa ɗanyen mai da ake bai wa matatun cikin gida, ciki har da matatar Dangote.
A cewarsa, “A ɗauki aƙalla kashi 60 cikin ɗari na waɗannan kuɗaɗe domin rage farashin samar da mai.”
Ya ƙara da cewa, “Idan aka tallafa wa ɗanyen mai kai tsaye, ba za a iya yin almundahana ba, kuma hakan zai kawo sauƙi nan take ga farashin kayayyakin mai.”
Ƙungiyar ta kuma buƙaci a ɗauki matakai na daidaita darajar naira domin rage tsadar kayayyaki a Najeriya.
TUC ta ce za ta miƙa shawarwarinta ga gwamnatin tarayya domin ganin an ɗauki matakin gaggawa.