Ɓangaren jam’iyyar PDP da ke ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike ya buƙaci mambobinsa da su yi watsi da wani taro da ɓangaren Taminu Turaki ya yi da jam’iyyar ADC.
Kakakin ɓangaren na ƙasa, Jungudo Mohammed, ya ce taron ba shi da izini daga PDP.
A cikin wata sanarwa, ya jaddada cewa jam’iyyar ba ta taɓa yin wata tattaunawa da ADC ba, yana mai cewa waɗanda suka halarci taron sun yi hakan ne a matsayin kansu.
Ya ƙara da cewa, “Wannan iƙirari ba shi da tushe kuma ba ya wakiltar matsayar jam’iyya.”
Taron dai ya gudana ne a tsawon sa’o’i biyu a Abuja, inda aka tattauna batutuwan ƙasa da haɗin gwiwar jam’iyyu gabanin zaɓen 2027.
Manyan ƴan siyasa ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Kwankwaso sun halarci tattaunawar.
Haka kuma, an samu halartar tsofaffin gwamnoni da manyan ƴan siyasa, wanda ya ƙara janyo hankali kan yiwuwar samun sabon haɗin gwiwar siyasa.
Sai dai ɓangaren Wike ya dage cewa, PDP na mai da hankali kan shirye-shiryen zaɓen fidda gwani ne a yanzu.
Ya ce za a sanar da jadawalin zaɓen cikin gida da ƙa’idoji nan gaba, yana mai jaddada ƙudurin jam’iyyar wajen samar da shugabanci nagari ga ƴan Najeriya.