Wasu ƙungiyoyi masu aikata laifuka sun mayar da hasumiyoyin sadarwa a Najeriya tamkar wuraren da akai musu ajiya don ɗiba, inda suka sace muhimman kayayyakin lantarki guda 656 a jihohi 14 a shekarar 2025 kaɗai, kamar yadda rahoton Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ya nuna.
Rahoton ya bayyana cewa, an sace injinan wutar lantarki guda 152 da batir 504 daga wuraren sadarwa, tare da ƙarin satar dizal sau 1,344 da kuma yawan yanke wayoyin fibre har sau 1,100 a mako zuwa ƙarshen shekarar.
Jihohin da suka fi fama da wannan matsala sun haɗa da Delta, Rivers, Legas, Kaduna da Abuja, inda ƴan daba ke kai farmaki kan hasumiyoyi suna kwasar kayayyaki kamar kebura, batira, na’urorin lantarki da man dizal domin sayarwa.
Lamarin bai tsaya ba, domin a farkon 2026 ma an sake sace batira 64 da injina 17 cikin watanni biyu kacal.
Shugaban ƙungiyar masu gudanar da harkokin sadarwa, Gbenga Adebayo, ya ce wannan matsala na hana ci gaban tattalin arziƙin dijital, yana mai cewa, “Waɗannan kayayyaki ba kayan aiki ba ne kawai, su ne ginshiƙin tattalin arziƙinmu da tsaron ƙasa.”
Kamfanin MTN Nigeria ya bayyana cewa ya kashe kusan naira biliyan 1 wajen inganta hanyoyin sadarwa, amma lalacewar kayayyaki na ci gaba da rusa nasarorin da aka samu.
Babban jami’in fasaha na kamfanin, Yahaya Ibrahim, ya ce, “Mun zuba jari sosai, amma a lokaci guda ana lalata kayanmu akai-akai.”
Ya ƙara da cewa, MTN na kashe kusan naira biliyan 7 a kowace shekara wajen gyaran fibre kawai, kuɗin da zai iya amfani wajen faɗaɗa ayyukanta.
Masana sun ƙiyasta cewa, lalacewar kayayyakin sadarwa ta jawo asarar kusan naira biliyan 14 ga kamfanoni a 2023.
Duk da cewa gwamnati ta ayyana kayayyakin sadarwa a matsayin muhimman kadarorin ƙasa, alƙaluman 2026 sun nuna cewa, matsalar na ƙara ƙamari.
Masana sun yi gargaɗin cewa, idan ba a ɗauki matakan tsaro ba, wannan matsala za ta ci gaba da durƙusar da harkokin sadarwa a Najeriya.