Gwamnatin Najeriya ta fitar da gargaɗi kan yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi da zai iya haddasa ambaliya a wasu yankuna na jihohi goma tsakanin ranar 8 zuwa 12 ga Afrilu, 2026.
Wannan sanarwa ta fito ne daga Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Kasa ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, kamar yadda takardar hasashen ambaliya mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Afrilu ta bayyana.
A cikin sanarwar da Daraktan Sashen Kula da Zaizayar Ƙasa, Ambaliya da Yankunan Gaɓar Teku, Usman Bokani, ya sanya wa hannu, an ce, “Waɗannan wurare da kewayensu na iya fuskantar ruwan sama mai ƙarfi wanda zai iya janyo ambaliya a cikin lokacin hasashen.”
Jihohin da ake hasashen za su fuskanci wannan yanayi sun haɗa da Ebonyi, Anambra, Ogun, Taraba, Cross River, Benue, Imo, Delta, Rivers da kuma Abia.
A jihar Ebonyi, an ambaci Afikpo da Nkalagu, yayin da a Anambra aka lissafa Atani, Iyowa Odekpe, Odekpe da Onitsha.
Haka kuma, wuraren Ayetoro da Ilaro a Ogun; Donga, Kwata Kanawa, Lau, Serti, Takum da Yorro a Taraba; da Edor, Ikom da Itigidi a Cross River na daga cikin yankunan da za su iya fuskantar wannan barazana.
Sauran wuraren sun haɗa da Igumale a Benue; Nworievbi, Okigwe, Otoko da Owerri a Imo; Oko Anara a Delta; Port Harcourt a Rivers; da Umuahia a Abia.
Ma’aikatar ta jaddada cewa waɗannan wurare da kewayensu na iya fuskantar ruwan sama mai yawa da “ka iya haifar da ambaliya” a cikin kwanakin da aka ƙayyade.
A karshe, ma’aikatar ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakan kariya domin rage illolin da ka iya tasowa.