Bayan Gabatar da Ƙudirori 38 A Majalissa, Amadi Ya Raba Motoci, Miliyoyin Nairori da Taransifomomi ga Ƴan Mazaɓarsa

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Mbaitoli/Ikeduru ta Jihar Imo, Honarabul Injiniya Akarachi Amadi, ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin tallafawa al’ummarsa da nufin bunƙasa rayuwar jama’a da kuma inganta ababen more rayuwa a yankin.

A wajen taron da aka gudanar a ranar Lahadi, wanda ya ja hankalin manyan baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya, Amadi ya raba kayayyaki da tallafin da suka haɗa da tsabar kuɗi har naira miliyan 200, taransifoma 67, tarakta, motoci kirar SUV, bas, babura, babura masu ƙafa uku (tricycle), kayan aikin noma, takin zamani, janareta, injinan niƙa, buhunan shinkafa da injinan ɗinki, da dai sauransu.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin siyasa, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Tajudeen Abbas, wanda Honarabul Sulaiman Abubakar ya wakilta, tsohuwar Ministan Ci Gaban Matasa, Dakta Jamila Ibrahim, Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Imo, Honarabul Austin Onyedebelu, da kuma wasu ƴan majalisa da dama da kwamishinoni.

A cikin saƙonsa, Kakakin Majalisar ya yabawa Amadi kan yadda yake taka rawar gani wajen inganta rayuwar al’ummarsa.

Ya ce, “Majalisar Wakilai za ta ci gaba da goyon bayan irin wannan yunƙuri da ke haɓaka cigaban jama’a da ƙarfafa demokaraɗiyya.”

Da yake jawabi a wajen taron mai taken “Daga Hangen Nesa Zuwa Sakamako”, Amadi ya bayyana cewa sha’awar yi wa jama’a hidima ce ta sa ya tsunduma cikin ayyukan raya ƙasa.

Ya ce, “Amincewar al’umma ita ce babban jarin da nake da shi, kuma zan ci gaba da kare ta ta hanyar gaskiya, sadaukarwa da kuma sakamako mai ma’ana.”

Ya ƙara da cewa, burinsa shi ne tabbatar da cewa kowace murya a mazaɓarsa tana da daraja a dukkanin shawarwarin da yake yankewa.

A bangaren ilimi, ɗaruruwan ɗalibai sun riga sun amfana da tallafin karatu daga shirinsa, yayin da ya yi alƙawarin ƙara faɗaɗa shirin zuwa ga sababbin ɗalibai.

Ya bayyana cewa yana hangen makomar matasan yankin yanda za su zama likitoci, injiniyoyi, lauyoyi da masu ƙwarewa a fannin ƙirƙire-ƙirƙire.

A cewarsa, “Ilimi shi ne makami mafi ƙarfi wajen yaƙar talauci,” inda ya ƙara da cewa duk ɗalibin da ya samu maki sama da 200 a jarabawar JAMB zai samu damar shiga shirin tallafin karatu a jami’o’in gwamnati a faɗin Najeriya.

A ɓangaren samar da wutar lantarki, Amadi ya sanar da rabon taransifoma 67 ga al’ummomi 63 masu cin gashin kansu a yankin.

Ya jaddada cewa, “Lantarki ba jin daɗi ba ne kawai, wajibi ne don bunƙasar tattalin arziƙi. Idan wuta ta inganta, kasuwanci zai bunƙasa, ilimi kuma zai inganta.”

Baya ga haka, shirin ya kuma mayar da hankali kan ƙarfafa ƙananan ƴan kasuwa da masu sana’o’i ta hanyar bayar da jari, kayan aiki da kuma horo domin tabbatar da dogaro da kai.

Amadi, ya kuma bayyana cewa wannan shiri ba kawai rabon tallafi ba ne, illa wani tsari ne na dogon lokaci da ya riga ya fara samar da sauyi a mazaɓar.

Ya lissafo wasu ayyuka da aka riga aka kammala da suka haɗa da ginawa da gyaran ajujuwa sama da 20, kafa cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu, cibiyar koyon sana’o’i, rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, da kuma shirin “Light Up Mbaike”.

A ɓangaren ayyukan majalisa, Amadi ya ce ya gabatar da ƙudirori 38 da ke matakai daban-daban a Majalisar Wakilai, yana mai cewa hakan wani ɓangare ne na gudummawarsa wajen samar da dokoki da za su inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Ya ƙara da cewa, “Burina shi ne kafin ƙarshen wa’adina, kowace al’umma a Mbaitoli da Ikeduru ta amfana da aƙalla aiki guda ɗaya mai amfani.”

Rahotanni sun nuna cewa shirin ya samu karɓuwa sosai daga al’ummar yankin, inda da dama suka bayyana shi a matsayin wata sabuwar hanya ta tabbatar da samar da ci gaba mai ɗorewa.

AmadiMajalisaTallafi
Comments (0)
Add Comment