Rikicin ADC Ya Ƙara Tsananta, Wani Sabon Tsagin Ya Bayyana, Ya Yi Watsi Da Tsagin David Mark Da Na Nafiu Gombe

Wani ɓangare a jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na 2023, Dumebi Kachikwu, ya sanar da shirin gudanar da babban taron ƙasa na jam’iyyar domin zaɓen sabon shugabanci.

An bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da kakakin sabon tsagin, Norman Obinna, ya yi a Abuja bayan wani zaman gaggawa na kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC).

Obinna ya ce zaman ya samu halartar shugabannin jihohi da sauran mambobin NEC, inda aka tattauna rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.

Ya bayyana cewa an riga an cimma matsaya ta hanyar sasanci cewa, dole a gudanar da babban taron ƙasa domin sabunta shugabanci, amma har yanzu hakan bai tabbata ba kusan bayan shekaru.

“Babban abin da aka cimma a sasancin shi ne a gudanar da babban taro domin zaɓen sabon shugabanci, amma har yanzu ba a aiwatar da hakan ba,” in ji shi.

Ya kuma zargi tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, da ƙoƙarin miƙa shugabancinta ga mutanen da ba ƴan jam’iyyar ba.

Tsagin ya ce ya shigar da ƙara a kotu domin ƙalubalantar waɗannan matakai, yana mai jaddada cewa NEC ce har yanzu ke da cikakken ikon jagorancin jam’iyyar.

Ya kuma nesanta kansa daga wata haɗaka ta haɗin gwiwa da ke ɗauke da manyan ƴan siyasa ciki har da David Mark da Rauf Aregbesola.

“Duk wani mataki da suka ɗauka a sunan ADC ba shi da inganci,” in ji Obinna.

Haka kuma ya ƙaryata iƙirarin Nafiu Bala Gombe na riƙe wani muƙami a jam’iyyar.

Tsagin ya sanar da kafa shugabanci na wucin gadi tare da roƙon INEC ta ba su sahalewa domin ceton jam’iyyar daga rugujewa.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin cikin gida ke barazana ga shirye-shiryen jam’iyyar na tunkarar zaɓen 2027.

ADCNajeriyaSiyasa
Comments (0)
Add Comment