ADC a Katsina Ta Shirya Taron Zaɓen Shugabanni, Ta Caccaki Gwamnatin Tinubu Kan Tattalin Arziƙi

Jam’iyyar ADC a Jihar Katsina ta gudanar da wani taron shugabanni domin shirya zaɓukan cikin gida gabanin babban taron ƙasa da jam’iyyar ta shirya gudanarwa a ranar 14 ga Afrilu, 2026.

Taron ya gudana a Paramount Event Center tare da halartar wakilai daga dukkan mazabu 361 na jihar.

Tsohon ɗan takarar gwamna na APC, Mustapha Inuwa, ya bayyana cewa za a fara zaɓukan daga ranar 9 ga watan Afrilu daga matakin rumfar zaɓe zuwa jiha.

Ya ce an shirya taron ne domin tattauna yiwuwar yin sulhu a zaɓen cikin gida.

“Ina ganin za mu iya yin sulhu domin idan gwamnati mai ci ba ta iya gudanar da zaɓe kai tsaye ba, mu a matsayin ‘yan adawa za mu iya,” in ji shi.

Ya bukaci ‘yan jam’iyyar su kasance masu natsuwa da haɗin kai.

Inuwa ya kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ta durƙusar da tattalin arzikin Arewa.

Ya ce: “A yau dole ne mutum ya sayar da buhunan masara uku kafin ya sayi buhu ɗaya na gari.”

Ya ƙara da cewa matsalolin tsaro da talauci sun jawo koma baya a ilimi da noma a yankin.

 Duk da haka, ya yi alƙawarin cewa idan ADC ta samu nasara, za ta inganta tsaro da tattalin arziki tare da yaƙi da cin hanci.

ADCKatsinaZabe
Comments (0)
Add Comment