“Mahaukaci Mai Hatsari Ga Tsaron Ƙasa,” Ƴan Majalisar Amurka Ga Trump Kan Yaƙi Da Iran

Wasu ƴan majalisa ƴan Democrat a Amurka sun yi Allawadai da Shugaba Donald Trump kan sabuwar barazanar kai hari kan cibiyoyin fararen hula a Iran, kamar yanda kafar Al Jazeera ta rawaito.

Trump ya yi wannan barazana ne a wani sako mai cike da kalamai masu zafi a ranar Lahadin Easter.

Ya ce zai kai hari kan tashoshin wutar lantarki da gadoji idan Iran ba ta buɗe mashigin Hormuz ba.

Ƴar majalisa Yassamin Ansari ta kira shi “mahaukaci mai hatsari ga tsaron ƙasa,” tana mai kiran a tsige shi daga mulki.

Haka kuma wasu ƴan majalisa sun bayyana kalamansa a matsayin abin kunya.

Sanata Elissa Slotkin ta ce kai hari kan fararen hula zai karya dokokin yaƙi na duniya.

Shi ma Sanata Bernie Sanders ya buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin nan take.

Sai dai wasu ƴan jam’iyyar Republican sun goyi bayan Trump, suna cewa yana da haƙƙin kare muradun Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 2,000 sun mutu a Iran tun bayan fara yaƙin.

Al JazeeraAmurkaIranTrump
Comments (0)
Add Comment