Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani tsari na biyan bashin da ya kai Naira tiriliyan 3.3 domin warware matsalolin da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki a ƙasar.
Wannan mataki, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana, shi ne mafi girman ƙoƙarin gyaran tsarin wutar lantarki da aka taɓa yi cikin shekaru da dama.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan adawa a ƙasar ke ci gaba da kiran masu zaɓe da kar su ƙara amincewa da Tinubu, musamman ganin yanda ya kasa cika alƙawarin samar musu wadatacciyar wutar lantarki da yai.
A cewar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, shirin ya shafi basussukan da aka tara tsakanin shekarar 2015 zuwa 2025, wanda ya haɗa da gwamnatoci uku.
Ya ce tuni kamfanonin samar da wutar lantarki guda 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar naira tiriliyan 2.3 daga cikin kuɗin.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta riga ta tara naira biliyan 501 domin aiwatar da shirin, inda aka riga aka fitar da naira biliyan 223, yayin da ake shirin fitar da sauran kuɗaɗe a tsarin bin matakai.
Najeriya dai na fama da ƙarancin wutar lantarki duk da yawan al’ummarta da ya haura miliyan 220.
Masana sun bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen inganta samar da gas ga tashoshin wuta, wanda zai ƙara yawan samar da wutar lantarkin.
Olu Arowolo-Verheijen, mai ba shugaban ƙasa shawara kan makamashi, ta ce, “Wannan ba kawai biyan bashi ba ne, sai dai dawo da amincewa a ɓangaren wutar lantarki.”
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da aiwatar da wasu gyare-gyare kamar ƙara yawan na’urorin mita da daidaita kuɗin wuta daidai da ingancin abin da ɗan ƙasa ya mora.
Haka kuma, an ba da fifiko ga kamfanoni da masana’antu wajen samar musu da wuta domin bunƙasa tattalin arziƙi.
Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa nasarar wannan shiri za ta dogara ne kan yadda za a aiwatar da shi da kuma yadda gwamnati za ta iya ci gaba da biyan kuɗaɗen duk da matsin tattalin arziƙi.