‘ADC Ba Ta Cika Da Matsala Ba’ — Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Kare Jam’iyyar Duk da Rikici

Mai son tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Abayomi Rotimi, ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi jam’iyyar duk da rikicin shugabanci da ke addabarta.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Litinin.

Rotimi ya ce babu wani abu da yake da cikakken muni ko alheri, yana mai jaddada cewa duk da matsalolin da ake gani a ADC, har yanzu akwai damar gyara.

“Ina cikin masu ganin cewa babu wani abu da yake da cikakken muni ko alheri. Don haka za mu iya aiki da wannan tsari,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa yawancin rikice-rikicen da ke cikin jam’iyyar sun samo asali ne daga kanta, amma za a iya magance su cikin gaggawa.

“Shugabanni dole su warware matsalolin cikin sa’o’i 72, in ba haka ba za mu fita,” ya yi gargaɗi.

Rotimi ya soki yadda wasu ke raina wasu a cikin jam’iyyar, yana mai cewa hakan na kawo tsaiko ga haɗin kanta.

“Ba za ka raina mutane ba sannan ka sa ran za su ci gaba da aiki tare da kai,” in ji shi.

Ya danganta burinsa na shugabancin ƙasa da buƙatar samun shugabanni masu tausayi da fahimtar jama’a.

Haka kuma ya bayyana aniyarsa na haɗa kan matasan Najeriya domin samar da tafiya mai ƙarfi, duk da cewa ya ce wasu na da wata manufa ta daban.

A halin yanzu, Hukumar INEC ta dakatar da hulɗa da ADC har sai an kammala shari’ar da ke gudana kan shugabancinta.

ADCINECZabe
Comments (0)
Add Comment