Oman da Iran Sun Tattauna Hanyoyin Buɗe Mashigin Hormuz Yayinda Yaƙi Ke Ci Gaba

Ƙasashen Oman da Iran sun gudanar da ganawar mataimakan ministocin harkokin wajensu domin tattauna hanyoyin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin sauƙi a mashigin Hormuz.

A cewar Al Jazeera, an gudanar da taron ne tare da ƙwararru daga ɓangarorin biyu.

Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Oman ta ce an tattauna hanyoyi daban-daban na tabbatar da zirga-zirga duk da halin da yankin ke ciki.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jiragen Oman uku sun ratsa mashigin a wani yanayi na daban, kusa da gaɓar ƙasar Oman.

Wannan na zuwa ne yayin da Iran ke taƙaita zirga-zirga tun bayan yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara a kanta.

Mashigin Hormuz na da matuƙar muhimmanci ga safarar mai da iskar gas zuwa Turai da Asiya.

Masana sun ce duk wani rikici a yankin na iya jefa kasuwar makamashi ta duniya cikin tashin hankali.

Wani masani, Amin Saikal, ya gargaɗi cewa faɗaɗa rikicin “zai jefa yankin cikin bala’i”, yana mai kira ga sasanci.

A halin yanzu, ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya domin warware matsalar.

HormuzIranOman
Comments (0)
Add Comment