Atiku Da ADC Sun Yi Allawadai Da Barazanar Da Wike Ya Yi Wa Ɗan Jarida, Sun Nemi Ya Gaggauta Neman Afuwa

Jam’iyyar ADC da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi kakkausar suka ga kalaman Ministan Abuja, Nyesom Wike, inda ya yi barazanar harbe ɗan jarida Seun Okinbaloye.

Wannan ya biyo bayan wata muhawara a shirin Politics Today inda Okinbaloye ya nuna damuwa kan yiwuwar komawar Najeriya mai bin tsarin jam’iyya ɗaya.

Wike ya ce “da zan iya karya allo, da na harbe shi,” yana zargin ɗan jaridar da nuna ɓangaranci.

Sai dai daga baya ya ce ba yana nufin kashe shi ba ne, illa ya nuna fushinsa ne kan kalaman da aka yi a talabijin.

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana wannan furuci a matsayin “abin Allawadai da rashin tausayi,” yana mai cewa dole ne a kare ƴancin faɗin albarkacin baki.

Haka kuma, ofishin yaɗa labarai na Atiku ya ce, wannan barazana na nuna yadda gwamnati ke ƙara nuna rashin juriya ga masu sukar ta.

Sanarwar ta ce, “wannan ba wasa ba ne, barazana ce kai tsaye ga ƴancin ƴan jarida,” tare da gargaɗin cewa, hakan na iya jefa demokaraɗiyya cikin haɗari.

Atiku ya buƙaci Wike da ya nemi afuwa nan take tare da gwamnati ta tabbatar da kare lafiyar ƴan jarida a Najeriya.

Masu sharhi sun ce wannan rikici na nuna ƙaruwar taƙaddama tsakanin gwamnati da ƴan adawa, yayin da ake fargabar taƙaita ƴancin kafafen yaɗa labarai a ƙasar.

ADCAtikuWike
Comments (0)
Add Comment