Ƴan Sanda Sun Kama Mutane Huɗu Da Zargin Kisan Gilla Wa Wani Kan Saɓani a Katsina

Rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a wani kisan gilla da ya yi sanadin mutuwar wani KC Joe a ƙauyen Kokami.

Kakakin rundunar, Abubakar Sadiq, ya ce ana ci gaba da bincike yayin da ake tsare da waɗanda ake zargin.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga saɓani tsakanin mamacin da wani Ibrahim Auwal, wanda aka ce ya mutu bayan an caka masa wuƙa.

Bayan samun labarin mutuwarsa, wasu fusatattun matasa sun kai farmaki kan Joe, suka kashe shi tare da ƙona gawarsa.

Kwamishinan tsaro na jihar, Dakta Nasir Mu’azu Danmusa, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa, “ba za a bar kowa ya ɗauki doka a hannunsa ba”.

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa za a hukunta duk waɗanda ke da hannu a lamarin.

Gwamna Dikko Radda ya yi kira ga al’umma su rungumi zaman lafiya musamman a lokacin bikin Easter, yana mai cewa, “haɗin kan addinai shi ne ginshiƙin ci gaba”.

Hukumomi sun ƙara tsaro a yankin domin kaucewa ƙarin tashin hankali.

KatsinaNajeriyaTsaro
Comments (0)
Add Comment