JAMB Ta Ƙaryata Jita-Jitar Ɗage Jarabawa, Ta Kira Sanarwar Da ‘Mugun Nufi’

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, JAMB, ta ƙaryata wata sanarwa da ke yawo cewa an ɗage jarabawar UTME ta 2026, tana mai bayyana ta a matsayin ƙarya da mugun nufi.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta buƙaci ɗalibai da su yi watsi da wannan rahoto, tana mai cewa bai fito daga gare ta ba.

Sanarwar ta ce, “an ja hankalinmu kan wata sanarwa ta ƙarya da ke cewa an ɗage jarabawar UTME 2026, muna sanar da jama’a cewa wannan labari ba gaskiya ba ne”.

JAMB ta tabbatar da cewa duk shirye-shiryen jarabawar na tafiya yadda aka tsara, inda aka sanya ranar gudanar da ita daga 16 zuwa 25 ga Afrilu, 2026.

Hakan na zuwa ne bayan gudanar da jarabawar gwaji (mock) a ranar 28 ga Maris, wadda ta fuskanci matsalolin fasaha a wasu cibiyoyi.

Daga cikin ɗalibai 224,597 da suka yi rajista, 152,586 ne suka samu damar rubuta jarabawar a cibiyoyi 989.

Hukumar ta ce, sama da cibiyoyi 20 an cire su daga tsarin saboda rashin inganci, tare da gargaɗin ɗalibai kan masu damfara da ke alƙawarin ƙara musu maki, tana mai cewa hakan laifi ne mai mai girma.

IlimiJAMBJarabawaNajeriya
Comments (0)
Add Comment