Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Zargin Sagagi, Ta Ce Abba Na Da Ƙarfin Gwiwa Da Karɓuwa A Wajen Jama’a

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaryata kalaman tsohon kwamishinan zuba jari, kasuwanci da masana’antu, Shehu Wada Sagagi, tana mai cewa zarginsa kan matakin siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba shi da tushe.

A cikin sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Juma’a, gwamnatin ta ce zargin cewa gwamnan ya sauya sheƙa ne saboda tsoron rasa tikitin wa’adi na biyu ƙarya ne.

Sanarwar ta bayyana cewa, wannan iƙirari wani yunƙuri ne na yaudarar jama’a da karkatar da gaskiya kan manufar gwamnan.

Ta jaddada cewa matakin da gwamnan ya ɗauka ya samo asali ne daga buƙatar samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.

Gwamnatin ta ƙara da cewa, wannan tsari wata dabara ce ta ƙarfafa haɗin gwiwa domin tabbatar da cewa alfanun mulki ya kai ga dukkan al’umma.

Ta kuma musanta cewa gwamnan na fargabar makomarsa ta siyasa, tana mai cewa yana da ƙarfin gwiwa da karɓuwa a wajen jama’a.

A ƙarshe, ta buƙaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan kalamai, tana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofin “Kano First” ba tare da wata tangarɗa ba.

Jam'iyyaKanoSiyasa
Comments (0)
Add Comment